Ya ce ya mika wa lauyoyinsa sunayen masu yada labaran karyar domin daukar matakin shari’a.
washington dc —
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya musanta rade-radin cewa ya fice daga APC tare da sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Da yake martani game da rade-radin a shafinsa na X, El-Rufa’i ya bukaci al’umma su yi watsi da jita-jita da karerayin da ake yadawa game da kawancensa na siyasa.
Ya kara da cewa ya mikawa lauyoyinsa sunayen masu yada labaran karyar domin daukar matakin shari’a.
“Don Allah ku yi watsi da karerayi da jita-jitar da ake yadawa a kan kawancen siyasata. Na mikawa lauyoyina bayanan masu yada labaran karyar domin daukar mataki na gaba,” kamar yadda ya wallafa a jiya Lahadi.