Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai bar Legas a yau 6 ga watan Janairun da muke ciki zuwa Accra, babban birnin Ghana, domin halartar bikin nadin zababben shugaban kasar John Mahama a gobe 7 ga Janairun 2025.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Lahadi.
An sake zaben Mahama, wanda ya kasance shugaban kasar Ghana na 12 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2017, a watan Disamban 2024. Shi zai gaji Shugaba Nana Akuffo-Addo (wanda ya mulki kasar daga 2017 zuwa 2025).
Tinubu, a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS ta raya kasashen afrika ta yamma, zai hadu da shugabannin kasashen Afirka a bikin.
A cewar Onanuga, karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya ne za su marawa Tinubu baya a tafiyar.
Dandalin Mu Tattauna