EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Wutar Lantarki Bisa Zargin Almundahana

Sale Mamman, tsohon ministan wutar lantarki

Ministan ya na tsare a wajen hukumar domin  a masa tambayoyi da kuma bincike.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Sale Mamman, tsohon ministan wutar lantarki a Najeriya, bisa zargin almundahana da ya kai Naira biliyan 22.

Jaridar Vanguard ta ce ta fahimci cewa kama shi na da nasaba da binciken da Hukumar ke yi kan almundahana a wasu ayyukan wutar lantarki.

EFCC

Bayanai sun nuna cewa ana zargin Mamman da hada baki da jami’an ma’aikatar da ke kula da asusu na ayyukan wutar lantarki na Zungeru da Mambilla tare da karkatar da kudaden da suka raba a tsakaninsu.

A cewar majiyoyi makusanta ga binciken, an gano wasu kadarori da ake zargin an samu tare da kudaden ne a Najeriya da kasashen ketare da ke da alaka da wadanda ake zargin, yayin da aka kwato miliyoyin Naira da Dalar Amurka.

Vanguard dai ta ce bata samu kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ba, domin jin ta bakinsa a kan wannan labarin.

Kamen ya kara jaddada kokarin hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa da kuma dorawa jami'an gwamnati alhakin ayyukansu.

Ministan ya na tsare a wajen hukumar domin a masa tambayoyi da kuma bincike.