Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kama wani tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode a Legas.
WASHINGTON —
An dai ce ana binciken Fani-Kayode bisa zarginsa da yin magudi da kuma canza wasu takardu kamar yadda wasu majiyoyi a Najeriya suka bayyana.
An dai kai tsohon ministan wanda ya koma jam’iyya mai mulki a Najeriya All Progressives Congress -APC a watan Satumba ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na shiyyar Legas jiya Talata.
Har yanzu ba a bayyana zarge-zargen ba amma kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Fani-Kayode da jami’an tsaro suka yi.
Fani-Kayode dai ya dade yana fafatawa da hukumar EFCC kuma an taba tsare shi na tsawon kwanaki 67 a shekarar 2016 tare da tsohuwar ministar kudi Nenadi Usman.