Ibrahim Magu ya yi wannan kiran ne a lokacin da hukumarsa ta shirya wani maci na tuna ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya a birnin Abuja. Najeriya kamar sauran kasashe masu tasowa tana fama da matsalolin cin hanci da rashawa lamarin da ke yiwa ci gaban kasar tarnaki.
Shugaban na EFFC, hukumarsa tana samun nasara domin galibin yan Najeriya na fahimtar aikin hukumar sai dai yan kalilan. Yace hukumarsa ta kara ilmantar da al’ummar kasa a kan cewa matsalar rashawa tana shafan kowa haka zalika shawo kanta na bukatar hadin kan kowa.
A hirarsa da wakilin mu Umar Faruk Musa, shugaban EFCC ya yi masa bayani cewa jami’an gwanmati da aka zargesu da aikata laifin rashawa za a gabatar da su gaban kotu idan aka tabbatar da laifinsu. Sai dai yace hukumarsa tana zurfafa bincike kuma ta tattara shaida masu sahihanci don haka take dadewa wurin gudanar da bincike.
Your browser doesn’t support HTML5