A ranar 13 ga wannan wata na Fabarairu ne babbar kotun tarayya dake Kano ta bada izinin mallakawa gwamnatin tarayya kudaden da hukumar EFCC ta gano a gidan Andrew Yakubu.
Sai dai lauyan Andrew yakubu, Barista Ahmed Raji, ya gabatarwa kotun bukatar soke hukuncin da kotun ta yanke, yana mai cewa hukumar EFCC ba ta cika sharuddan da doka ta gindaya ba.
Masana harkokin shari’a da dokoki ‘kasa suka fara bayyana ra’ayinsu dangane da wannan batu, inda suke ganin wannan lamari ya zamanto abin takaici kan cewa daga karshe doka ka iya sa a maidawa wanda ake zargin da aikata lefi kudadan da aka kwato. A cewar Barista Abdullahi Bulama.
Shi kuma Barista Abdul Adamu Fagge, shawara ya baiwa hukumomin da rashawa a Najeriya, kan bukatar zurfafa bincike a kowanne sha’ani gabannin mika shi ga kotu.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5