Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan JTF Ya Musanta Zargin da Wata Jarida Ta Yiwa Shugaban 'Yan Bangan


Barrister Jibrin Gunda, lauyan dake ba JTF shawara
Barrister Jibrin Gunda, lauyan dake ba JTF shawara

Wata jarida mai suna Desert Herald ce ta ruwaito cewa an kama shugaban JTF saboda wai an gano ya mallaki gidaje da dama da shanu wajen dari biyar da dai wasu dukiyoyi

Barrister J. T. Gunda wanda shi ne yake ba Civilian JTF shawara akan harkokin shari'a shi ya kira taron manema labarai cikin gaggawa domin ya yiwa duniya bayanin abun da yace shi ne gaskiya game da JTF.

Yace sun karanta a jaridar Desert Herald wai an kama shugaban JTF saboda yana da shanu dari biyar a wani fili da ya saya, yana da gidaje kusan 20, yana da wani makeken gida a Abuja. Wai da kuma aka je bincike a gidansa an samu tsabar kudi miliyan dari biyar.

Inji Barrister Gunda suna karyata wannan zargin da jaridar tayi amma ba wai suna goyon bayan wani mai laifi ba ne. Yace idan shugaban yayi laifi dole ne hukuma tayi aiki a kansa. Yace amma harsashen da jaridar tayi ba gaskiya ba ne. Idan kuma jaridar nada gaskiya ta fitar da shaida ko shaidu.

Shugaban da ake magana a kansa shi ne Baba Lawal Jafa wanda a lokacin da lauyan yake ganawa da manema labarai yana bakin aiki.

Dangane da cewa can baya sojoji sun kama wasu 'yan JTF da hannu cikin satar shanu sai lauya Jibrin Gunda yace tabbas akwai wadanda aka kama aka kuma tafi dasu. Yace lokacin da aka kamasu jami'an tsaro sun fada masu. Amma a wannan zargin babu abun da jami'an tsaro suka fada masu.

Inji Barrister Gunda wadansu ne da basa son abun da JTF keyi suke son su kawo baraka tsakaninsu da jami'an tsaro.

Sun ba jaridar kwana ukku ko ta fitar da shaida ko kuma ta nemi gafara a rubuce. Bayan kwana ukku idan har basu yi komi ba zasu gurfanar da jaridar gaban shari'a.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG