Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Editan Sashen Hausa Ya Bi Sawun Wadanda Rikicin Boko Haram Ya Shafa


Alhaji Aliyu Mustaphan Sokoto babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka yana yiwa wasu tambayoyi akan yadda rikicin Boko Haram ya shafesu
Alhaji Aliyu Mustaphan Sokoto babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka yana yiwa wasu tambayoyi akan yadda rikicin Boko Haram ya shafesu

Rikicin Boko Haram ya jawowa mutane musamman a arewa maso gabas mugun koma baya a harkokin yau da kullum da na tsaro da rayuwa da tattalin arziki.

Alkassim Ibrahim wani mai sana'r katifa a cikin Maiduguri kafin rikicin Boko Haram ya barke yace can baya sun shiga cikin bala'i har ma yawo cikin gari ya gagara saboda ta'adanci.

Yanzu kokarin da shugaban kasa yayi tare da gwamnan jihar Bornon ya sa ana iya yawo cikin gari ba tare da wani tsoro ba. Sun samu zaman lafiya kuma suna sana'arsu.

Saidai rashin maida jama'a kauyukansu idan sun yi kayansu babu inda zasu kai su sayar. Tsadar rayuwa kuma ta addabi kowa.

Kafin rikicin Boko Haram sukan yi kasuwanci da kasashen dake makwaftaka da Najeriya. Sadiq Musa yace a gaskiya sun samu matsala da wadanda suke shigowa daga waje. Rikicin ya sa sun y hasarar masu shigowa suna sayen kayansu daga Chadi da Kamaru da Nijar da Sudan da kasar Afirka ta Tsakiya. Yace duk abun da ya shafi Najeriya ya shafi kasashen saboda da Najeriya suke tinkaho. Ita Borno kanta tamkar cibiyar kasuwanci ce inda suke samun albarka ba kadan ba kafin rikicin.

Rikicin ya kawo karancin kaya inji Musa. Haka ma mutanen Yobe suka shaida an soma samun zaman lafiya domin zaman lafiyan Borno shi ne na jihar Yobe. Rikicin ya sa mutanensu sun fita gudun hijira musamman mutanen Buni Yadi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG