ECOWAS Zata Tura Tawagar Sulhu Zuwa Kasar Mali

Zaratan sojojin Mali su na samun horo daga wani sojan Amurkan tsaye a kan wata mota

Tawagar zata yi kokarin karfafa tattaunawa a tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen Abzinawa na arewacin kasar

Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta ce tana shirin tura tawaga zuwa kasar Mali domin karfafa tattaunawa a tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen Abzinawa na arewacin kasar, kafin zaben da ake shirin gudanarwa a wata mai zuwa.

Darektan sadarwa na kungiyar ECOWAS, Sonny Ugoh, ya fadawa VOA cewa kungiyarsu na son hada sassan biyu wuri guda domin tattauna musabbabin wannan tawaye, kuma su na da kwarin guiwar samun nasarar wannan shiga tsakani.

Yayi kira ga ‘yan kasar ta Mali da su goyi bayan wannan yunkuri, yana mai fadin cewa kasar tana bukatar tattaunawa ba wai zub da jini na babu gaira babu dalili tare da barnar dukiya ba.

A watan Janairu ne mayakan kabilar Abzinawa na arewacin Mali suka fara kai hari kan garuruwa da cibiyoyin gwamnatin kasar. Da yawa daga cikin mayakan sun koma gida ne daga kasar Libya a bayan da suka yi sojar haya wa marigayi shugaba Mu8ammar Gaddafi.

A watan da ya shige Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan fada a tsakanin gwamnatin Mali da ‘yan tawayen Abzinawa ya kori mutane kimanin dubu 130 daga gidajensu da garuruwansu zuwa makwabtan kasashe irinsu Jamhuriyar Nijar da Mauritaniya da kuma Burkina Faso.