ECOWAS Ta Maida Shugaban Burkina Faso Kan Karagar Mulki

Shugabannin ECOWAS a Taronsu a Abuja, Satumba 22, 2015.

Sojojin dake gadin fadar shugaban kasar suka amince, zasu koma barikokinsu

Shugaban rikon kwarya na kasar Burkina Faso Michele Kafando yace ya koma karagar mulki, mako guda bayanda dogarawan fadar shugaban kasa suka yi mashi juyin mulki.

Kafando ya shaidawa manema labarai yau Laraba cewa, an maido da gwamnatinsa, kuma ya kama aiki na take.

Tun farko yau, sojojin dake gadin fadar shugaban kasa suka amince, zasu koma barikokinsu a wata yarjejeniya da aka cimma bayanda shugabannin kasashen Senegal, Togo, Benin da kuma Najeriya, suka tafi Ouagaduougou babban birnin kasar domin tatttaunawa.

Dakarun gwamnati da suka yi dafifi a babban birnin kasar domin nuna adawa da shugabannin juyin mulkin sun amince zasu ja da baya, su nisanci babban birnin da tazarar kilomita hamsin.

Madugun juyin mulkin janar Gilbert Diendere ya nemi kasar gafara jiya Talata ya kuma yi alkawarin mika mulki idan shugabannin dake ganawa a Ouagaduougou suka bukaci ya yi haka. Tun farko ya shaidawa Muryar Amurka cewa, baya so a zubar da jinni.

A halin da ake ciki kuma, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta shawarci Amurkawa dake Burkina Faso su fice daga kasar dake Afrika ta yamma, ta bayyana rashin tabbas a fannin harkokin tsaro. Ta kuma bada shawara kada a tafi kasar dake cikin yanayin rudani.