ECOWAS Ta Ce Dakarantu Su Zauna Cikin Shirin Zuwa Nijar

Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)

Hafsoshin tsaron kasashen yankin yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS (Hoton AP/Chinedu Asadu)

A cewar Outtara, tura dakarun ECOWAS ba bakon abu ba ne, yana mai cewa, a baya an tura su kasashen Liberia, Saliyo, Gambia da Guinea Bissau.

Kungiyar Raya tattalin arzikin Afirka ta ECOWAS, ta umurci dakarunta da su zauna cikin shirin zuwa Jamhuriyar Nijar.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya ba da umurnin yayin da yake karanto matsayar karshe da kungiyar ta dauka a taronta.

Kungiyar ta gudanar da taron a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Alhamis don duba mataki na gaba da za ta dauka bayan da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka bijirewa wa’adin mako guda da kungiyar ta ba su don su maido da mulkin farar hula.

Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai bayan taron, Shugaban Ivory Coast, Alassane Outtara, ya kwatanta tsare Shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa a matsayin aikin ta’addanci.

“Kungiyar ECOWAS ba za ta lamunci wannan ba, wannan ba batu ba ne na cewa Najeriya na yakar Nijar, sam ba haka ba ne, matsayar da muka dauka ta ECOWAS ce, kuma ina fata za a aiwatar da ita ba da bata lokaci ba.

“Mun tura tawaga zuwa Nijar, mun tura Abdulsalami Abubakar, mun tura Sultan of Sokoto, mun tura tsohon gwamna (CBN) Sanusi wanda abokina ne, don su yi magana da al’umar Nijar, amma sun ci gaba da tsare Bazoum a matsayin wanda suka yi garkuwa da shi. Ni a nawa ganin, wannan aikin ta’addanci ne.”

A cewar Outtara tura dakarun ECOWAS ba bakon abu ba ne, yana mai cewa, a baya an tura dakarun kasashen Liberia, Saliyo, Gambia da Guinea Bissau.

“Yau kuma, mun tsinci kanmu da Nijar, ECOWAS ba za ta lamunci wannan ba.