Eagles Zata Lallasa Pharaohs Na Misra

Kungiyar Super Eagles ta Najeriya zata jefa kwallaye da yawa a ragar kungiyar Pharaohs ta Egypt a wasan su na shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2017 da kungiyoyin biyu zasu buga a ranar juma'a idan Allay ya kaimu sati mai zuwa a jahar Kaduna, kamar yadda Aaron Samuel ya fada.

A yau laraba ne dan wasan ya bayyana haka a shafin thenff.com cewar ko shakka babu jefa kwallaye a ragar Pharahos of Egypt ba wata matsala bace a arangamar da kungiyar zata yi da takwarar ta ta.

Cikin 'yan wasan da zasu buga wasan sun hada da shahararren dan wasan mai bugawa kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow FC a Rasha wasa, tare da Kaftin Ahmed Musa duk suna cikin 'yan wasa 21 wadanda kwac mai rikon kwarya Samson Siasia ya gaiyata dake bugawa wasu kungiyoyin kasashe wasa.

Ya kara da cewa "jefa kwallaye bazai taba zama da matsalaba idan muka yi ma Pharaohs of Egypt dirar maiki a Kaduna, domin kuwa muna da shahararrun 'yan wasan da suka fi na Egypt iya taka leda".

"Naji maganganun da 'yankungiyar suke yi wai baza mu iya doke su ba, nasan duk cika baki ne da kuma yin amfani da wata dama domin kashe mana gwiwa."

Ranar 25 na wannan watan ne kungiyar Super Eagles zata dauki bakuncin kungiyar ta Pharaohs of Egypt a jahar Kaduna Najeriya, kuma duka kungiyoyin zasu sake karawa bayan kwanaki hudu a filin wasa na Borg el-Arab, dake Alexandria.