Dusar Kankarar Ba Sabun Ba Ta Janyo Mace-Mace Da Katsewar Lantarki A Amurka

Wasu ma'aikata na kawar da dusar kankarar da ta tare hanya a wani yankin arewacin New Jersey

Dusar kankarar da yawan ta ya kai santimita 30 ta zuba a jahohin Pennsylvania da Connecticut da kuma New Jersey

A cikin wani al’amarin da ba kasafai aka saba ganin irin shi a cikin watan oktoba a nan Amurka ba, sai ga shi an yi dusar kankara a wasu jahohin arewa maso gabashin kasar wadda ta janyo mace-mace a wurare ukku sannan kuma ta haddasa katsewar wutar lantarki a gidaje da masana’antu fiye da miliyan biyu.

Dusar kankarar da yawan ta ya kai har santimita 30 ce ta zuba a wasu sassan jahohin Pennsylvania da Connecticut da kuma New Jersey, ta yi yawan da ya tilastawa jami’ai ayyana dokar ta baci a jahohin.

Haka kuma dusar kankarar ta yi matukar shafar sufuri inda a dole ta sa aka soke tashin jirage sama masu dimbin yawa, aka rurrufe wasu hanyoyin da motoci ke bi kuma aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa.

Wani mutum na tura wata motar da ta makale a cikin dusar kankara

Mace-macen da aka samu sun wakana ne sanadinyar hadura masu nasaba da dusar kankarar a jahohin Pennsylvania da Connecticut da kuma Massachussetts.

Jahar New Jersey na daga cikin wuraren da dusar kankarar ta yi muni, inda mutane fiye da dubu 650 su ka rasa wutar lantarki. Za a shafe kwanaki da dama kafin wutar lantarkin ta samu a duk fadin yankin mai jahohi da yawa.