Duk ‘Yan Najeriya Daya Su Ke a Wurinmu – Sojoji

Dakarun Najeriya sun ce kowane dan Najeriya daidai ya ke a idonsu ba sa nuna fifiko akan kowa a ayyukan da su ke yi na samar da zaman lafiya a arewa maso gabashin kasar.

Rundunar sojin ta fadi hakan ne a wani martani da ta mayar ga kungiyar da ke fafatukar ganin an kubutar da ‘yan matan Chibok ta Bring Back Our Girls, bayan da su ka nuna cewa Serah Luka, yarinyar da aka kubutar a baya-bayan nan ba ‘yar Chibok ba ce.

“Mutane su rika la’akkari da cewa duk ‘yan Najeriya daidai su ke a wurinmu,” inji Kakakin Sojin Najeriya Kanar Usman Kuka Sheka.

A baya ‘yan kungiyar ta Bring Back Our Girls sun zargi sojojin Najeriya da cewa suna riga malam masallaci domin ba sa tuntubarsu idan sun ceto wata yarinya.

“A cikin sojoji akwai mutane da ba sa san a ce mutane suna kawo gudunmuwa.” Inji daya daga cikin shugabannin ‘yan kungiyar.

Takaddama ta kaure ne a ‘yan kwanakin nan bayan da aka ceto Serah Luka, inda sojoji suka ce ‘yar Chibok ce, yayin da iyayen garin na Chibok da ‘yan kungiyar suka yi watsi da ikrari, suna masu cewa a iya bincikensu babu yarinya mai suna haka a jerin wadandan aka sace.

Wannan lamari dai ya sa masu lura da al’amura sun fara dasa alamar tambaya kan rashin maida hankali da ba a yi kan daruruwan mata da ‘yan mata har da ma maza da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka sace, wadanda har yanzu ba a san inda su ke ba, amma aka fi maida hankali kan 'yan matab Chibok.

Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka a Abuja Hassan Maina Kaina domin samun karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Duk 'Yan Najeriya Daya Su Ke a Wurinmu -2'21"