Wasu gwamnoni masu jiran gado na luna alamun yin binciken abubuwan da basu gamsu dasu ba daga wadanda zasu karbi mulki a hannun su.
Wannan bai rasa nasaba da labaran yadda wasu Gwamnonin jihohi zasu bar jihohinsu da bashin da wasu ya kai miliya dubu dari biyu.
A jihar Bauchi ma’akatan jihar na matukar jin jikin rashin biyan su albashi, in ji Gwamna mai jiran gado Barrister, M.A Abubakar.
Yace “a jihar Bauchi, kwana uku bayan an karbo Kason jihar daga Gwamnatin tarayyar Najeriya, watan da aka samu aka biya albashi kwana uku baya idan wata matsala ta milyan biyar ta tashi a jihar Bauchi ba za’a iya yin ta ba, duka makudan kudaden da aka karba a baya a yau a jihar Bauchi, kusan babu abunda zaka iya nunawa na irin wadannan kudaden.”
Ya kuma kara da cewar “duk da dai a baya bazan yi bincike na wannan Gwamnati mai baring ado ba, amma kuma nayi alkawarin cewa duk inda kudin jihar Bauchi yake da akayi almundahanarsa zan bi in Allah ya yarda sai an karbo shi.”