WASHINGTON D.C —
Matasa a jihar Kano sun bayyanawa Wakiliyar Muryar Amurka Baraka Ibrahim ra’ayoyinsu game da maganar cewa an ware wasu makuden kudaden Jihar don sallamar Gwamna da Mataikainsa da kuma sauran tawagarsu.
Wasu sun nuna cewa hakan bai dace ba domin kuwa akwai wasu ayyukan da ya kamata ace an yi ne ba a kwashe kudin garin ana biyan masu barin gadon ba. To amma da yake ra’ayi riga ne kowa da irin wacce yake saka wa kansa wasu bah aka suke gani ba.
A ganin wasu matasan shine, ai ba laifi ba ne don an salami Gwamnan Kanon Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da mukarrabansa ba, musamman in aka yi la’akari da yadda suka yiwa jihar aiki tukuru ba tare da wawushe kudin jihar ba. Don haka sun cancanci a sallame su da tukwici mai kyau.