Babban Kocin ‘yan wasan kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 23, Samson Siasia, ya ce suna cigaba da shirye shirye, gabanin wasan Olympics da za a yi shekara mai zuwa.
Kungiyar ‘yan wasan ta sami nasara akan Algeria inda suka yi masu ci biyu da daya ranar Asabar da ta gabata, hakan ya sa suka kasance zakarun kungiyar ‘yan kasa da shekaru 23 na wasan African championships da aka buga a Dakar babban birnin Senegal.
‘Yan wasan kuma za su wakilci Afrika a Rio, tare da Algeria da Afrika ta kudu.
“Ina mai farin cikin cin wannan kofin, duk da dai an ji jiki, amma muhimmin abu shine an yi nasara” a cewar Siasia.
Ya kuma ce abun ba mai sauki ba ne idan aka yi la’akari da ‘yan wasan da muka kara da su a zagayen farko da na biyu.
‘Yan wasan Algeria na da hazaka kuma sun nuna ta. Haka su ma ‘yan wasana, abinda ya sa muka sami nasarar cin wasan.
Yanzu za mu cigaba da yin shiri, tare da gyara kurakuranmu da kuma kara kwarewa.
Siasia, wanda ya jagoranci Najeriya a wasan Olympics din shekarar 2008, inda ta sami lambar azurfa, ya ce zai kara kokari a shekarar 2016.