Farinciki ko juyayi? Mr. Toni da matar sa Harold, na bukin cikar su shekaru goma sha biyu 12, da yin aure. A na cikin bukukuwan murnar auren, sai mijin nata ya turo ta daga saman wani dutse, nan take matar ta mutu. Amma abun tambaya a nan shine, ko menene dalilin yin hakan gare shi?.
Rahotani sun bayyana cewar yayi hakan ne akan dalilin yana so ya mallaki kudin inshorar rayuwar ta da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan uku da dubu dari biyu $3.2M dai-dai da naira milliyan dari bakwai da milliyan hudu 704,000,000. Hakan ya bayyana ne kwanaki kadan bayan mutuwar matar a yayin da yaje karbar kudaden.
Bayan jami’an ‘yan sanda sun zurfafa bincike, sun iya gano cewar Mr. Toni, a shekarar 1995, hakan ya faru da tsohuwar matar sa, wadda ta mutu batare da gano dalilan mutuwar ta ba. A lokacin dai ya bayyana cewar ita tsohuwar matar ta sa mai suna Sandra, na kokarin canza tayar mota sai tsau-tsayi ya abka mata, abun da ke rike da motar ya cire sai motar ta fado mata ta lamarin da yayi sanadiyyar rasuwar ta.
Dukkan matan sun mutu a dai-dai lokutan da babu wasu shaidu da zasu iya bayyana abin da ya faru a wajen. Yanzu dai yana tsare inda ake cigaba da tuhumar sa kafin a yake mashi hukunci dai-dai da laifin da da ya aikata.