Duk Abubuwan da Suke Faruwa Alamarin ne na Zuciya

A yayin da sabuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari, ke fafutukar shawo kan ‘yan kungiyar Boko Haram, a Najeriya, shuwagabanin addinai na ci gaba da bada shawarwarin gano bakin zaren.

Sarkin Malaman Jihar Neja,Alhaji Mamman Dan Mariga, yace gudanar da aduo’I, na masamman a kasar a dai dai wannan lokaci da rukicin Boko Haram, ke kara zafi nada matukar tasiri, yakara da cewa a nemi Malamai, Kiristoci da Musulmai wadanda zasu yi adu’a tsakanin da Allah, domin Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.

Amma sakataren kungiyar Kiristocin jihar Neja, Rev. Joshua, cewa yayi kamata yayi Malaman addinai su maida hankalin wajen cusawa jama’a, jin tsoron Allah, yace duk wanda bashi da tsoron Allah yafi dabba muni domin hankalinsa ba irin na mutun bane, yana mai cewa duk abubuwan da suke faru alamarin zuciya ne kuma ba wanda ya isa ya gyara zuciya sai Allah.