Dubun Dan Yahoo Ta Cika

A jiya ne wata kotu ta yanke ma wani matashi dan asalin kasar Canada hukuncin daurin gidan kaso na shekaru 5, biyo bayan zargin sa da aka yi na hada baki da wasu ‘yan kutse da suka yi a shekarar 2014, wanda suka shiga asusun mutane na Yahoo.

Kotun kuma ta yanke masa tarar da zai biya ta dalar Amurka, dubu dari biyu da hamsin, dai-dai da kwatancin Naira milliyan casa’in. Mr. Karim Baratov, wanda ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a watan Nuwambar shekrar 2017 a garin San Francisco, alkalin kotun mai shari’a Vince Chhabria, ya bayyana cewar matashin dan kasar Canada amma haifaffen kasar Kazakhstan ne.

An kama shi a kasar ta Canada a watan Maris 2017, lauya mai kare matashin yace hukuncin da aka yanke misa na gidan kaso na tsawon watannin 45, ya zuwa yanzu yayi watannin 94, matashin dai shine mafi karancin shekaru a cikin jerin matasa masu satar bayanai da aka kama.

A shekarar 2017 dai ma’aikatar shari’a ta Amurka ta tuhumi matashin da wasu matasa uku, kana da wasu ma’aikatan tsaro na kasar ta Canada don bada tasu gudunmawa ga matasan wajen satar bayanan jama’a a shafin Yahoo.