Dubun Ahmed Hassan Ta Cika

Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke wani matashi Ahmed Hassan, mai shekaru 26, dan asalin jihar Kaduna, kuma dalibi a jami’ar Caleb dake Imota a jihar Legas, da laifin yin Sojan gona.

Shi dai Ahmed Hassan, wanda yake shekara ta biyu ta zangon karatu a jami’ar inda yake karatun Architect masu ilimi fasalta gine gine, yayi Sojan gona ne cewar shi jami’in dakarun Sojan sama na Najeriya ne.

Dubunsa ta cika ne alokacin da aka kama wani Ibrahim Yahaya, mai sana’ar haya da mashin ko kuma okada, wanda yake aike harma da sayomasa muggan kwayoyi.

A ranar da aka kama shi ya aiki Yahaya ya sayo masa pakitin Codeine goma sha daya (11) da wata nau’in kwaya da ake kira Rohypnol.

Dake ake masa tambayoyi Ahmed, ya ce ya samu kayan jami’an tsaron ne daga wani abokinsa mai suna Rufa'i, ya ce yana amfani da kayan ne domin kada masu gadin makarantar su bincike shi duk lokaci da ya zo makaranta.

Ya kuma kara da cewa shi ke amfani da kwayar ba wai cewa yana sana’ar sayarda kwaya ba ne.

Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Legas, Edgal Imohimi, ya ce rundunarsa zata yi aiki tare da hukumar Sojojin sama domin damke duk masu taimakawa Ahmed jami’an tsaro ko fararen hula.

Hukumar makarantar har yanzu bata ce kala ba akan batun.