Wasu dubban 'yan Rasha sun jure ruwan sama mai sanyi su ka yi dafifi a wani dandalin tsakiyar birnin Moscow a daidai lokacin da kungiyoyin da ke adawa da su ke kokarin sake samun karfin gwiwa bayan kwashe tsawon lokacin bazarar 'summer' da aka yi ana ta zanga-zanga kan zabukan yankin da ma siyasar kasar dungurungum.
Gangamin na jiya Lahadi shine na babban yunkuri na farko da kungiyoyin siyasa na masu ra'ayin sassaucin da kuma jam’iyyu masu alaka da su tun bayan zaben da aka gudanar a farkon wannan watan. Abubuwan da su ka faru gabanin zaben na ranar 8 ga watan Satumba, musamman ma yadda wasu jami'an zabe su ka yi ta hana 'yan takarar bangaren adawa tsawaya takarar --- shi ne babban musabbabin wannan zanga-zangar ta kyamar gwamnati da aka dade ana yi, wadda an yi shekaru da dama ba a ga irinta ba.
Sai dai maimakon zabe, abin da ya fi aukuwa a ranar 29 ga watan Satumba shi ne “danniyar siyasa” a yayin da 'yan raji su ka bukaci da gwamnati ta dakatar da daukar matakin kai samame inda aka auna shugaban yan adawa da yake yaki da cin hanci da rashawa, Aleksei Navalny da kuma duka inda magoya bayansa suke a fadin kasar.