Banda 'yan kasuwan da 'yan Boko Haram suka kashe akwai wasu fiye da dubu hamsin da ta'adancin kungiyar ya karya,basu da jari ko kaya ko ma wurin tsugunawa su yi kasuwanci.
Hadakar kungiyar 'yan kasuwa ta Najeriya ta nemi taimako daga gwamnatocin jihohi da na tarayya.
Alhaji Muhammad Ibrahim 86 mataimakin shugaban 'yan kasuwan Najeriya mai kula da jihohin arewa 19 ya bayyana halin da 'yan kasuwan ke ciki.Yace sun tara alkaluman 'yanuwansu da rikicin ya shafa kuma zasu turawa gwamnonin jihohin Adamawa da Borno da Yobe.
Wadanda aka wargaza dukiyoyinsu sun dawo babu kaya babu shago ko jari. Ya kira gwamnatoci da su taimaka domin 'yan kasuwan su koma sana'arsu. Ibrahim 86 ya yi harsashen mutanensu da bala'in Boko Haram ya shafa sun kai dubu dari. Idan za'a bada taimakon a bayar kai tsaye domin gudun kada ya makale.
Saidai wasu gwamnonin sun fara tunanin taimakawa 'yan kasuwan. Gwamnan jihar Adamawa Sanata Bindow Umaru Jubirilla ya bayyana irin matakan da suke dauka domin taimakawa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5