Dubban yan kasar Bahrain sunyi gangamin neman canji

Dubban 'yan kasar Bahrain ke gangamin nuna rashin amincewa.

Dubban mutanen ne suka yi caa a titunan wajen baban birnin kasar Bahrain suna bukatar karin canje canje. Anyi zanga zangar ta jiya juma’a ce, a yayinda gwamnati da kungiyoyin masu hamaiya suke nazarin sauye sauyen da kwamitin da shugabanin kasar suka kafa ya gabatar.

Dubban mutanen ne suka yi caa a titunan wajen baban birnin kasar Bahrain suna bukatar karin canje canje. Anyi zanga zangar ta jiya juma’a ce, a yayinda gwamnati da kungiyoyin masu hamaiya suke nazarin sauye sauyen da kwamitin da shugabanin kasar suka kafa ya gabatar. An dai kafa wannan kwamiti ne domin ya bincike murkushe masu zanga zagar kin jinin gwamnati da aka yi harma aka kashe fiye da mutane talatin.

To amma sai aka samu koma baya a lokacinda jam’iyar Yan Shiya ta Al Wefaq jam’iyar masu hamaiya mafi girma ta fice daga wajen yin shawarwari tana mai fadin cewa ba da gaske gwamnati take na ganin a samun sahihan caje canje da kuma yin tattaunawa tsakani da Allah ba.

A ranar alhamis Sarki Hamad Bin Isa Al Khalifa yayi na’am da shawarwarin da kwamitin ya gabatar ciki harda baiwa Majalisar wakilai karin iko da kuma inganta kare hakki da yancin jama’a kasar. Haka kuma kwamitin ya bada shawarar a kafa ma’aikatar shari’ar mai zaman kanta