Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akasarin kwanadojin mayakan kasar Turkiya sunyi murabus


Hafsan mayakan kasar Turkiya, Janaral Isik Kosaner. (File)
Hafsan mayakan kasar Turkiya, Janaral Isik Kosaner. (File)

Kwamandojin mayakan kasar Turkiya duk sunyi murabus a yayinda tankiya ke kara kamari tsakanin gwamnatin kasar da mayakan kasar

Kwamandojin mayakan kasar Turkiya duk sunyi murabus a yayinda tankiya ke kara kamari tsakanin gwamnatin kasar da mayakan kasar. Jiya juma’a kafofin yada labarun kasar suka bada rahoton cewa hafsan mayakan kasar Janaral Isik Kosaner da kwamadojin rundunar soja dana mayakan ruwa da kuma na mayakan sama duk sun mika takardun yin murabus ga gwamnatin kasar.

Kafafin yada labaru sunce Janaral Kosaner ya bukaci yin murabus domin yana gani hakan ya zama wajibi. Wannan murabus ya biyo bayan ganawar da Kosaner yayi da Prime Ministan kasar Recep Tayyip Erdogan da kuma shugaba Abdullah Gul domin tattauna karawa wasu jami’an soja mukami a wajen taron Majalisar koli ta soja da za’a yi a makon gobe. Am bada rahoton cewa Mr Erdogan ya nuna alamar cewa zai hana a karawa jami’an sojan da ake zaton suna da hannu a makarkashiyar hambarar da gwamnati mukami.

.Tuni dama hukumomi ke tsare da fiye da mutane dari uku a zaman wani bangare na binciken da ake yi akan makarkashiyar da ake zargin ana kulawa domin tagulawa gwamnati al’amurra. Akwai kimamin jami’an soja harda wadanda suka yi ritaya maitan ciki harda masu mukaman Janaral talatin da ake caje su a binciken. Yawancin sojojin da aka caja suna tsare.

XS
SM
MD
LG