A can cikin daren jiya ne shugabannin majalisar wakilai ta Amurka suka bada sanarwar cewa an dage jefa kuri’a da aka shirya dangane shirin karawa Amurka ikon karbo bashi,da rage kudi da gwamnati take kashewa.
Da a jiya ne aka so kada kuriyar, amma kafofin yada labaran Amurka sun ambaci majiyoyi a majalsiar dokoki suna cewa an jinkirta muhawara da kada kuri’ar, domin shugabannin Republican suna neman karin goyon baya daga wakilan jam’iyyar ga kudurin da kakakin majalisa John Boehner ya gabatar.
Shirin na kakakin majalisar Boehner ya bukaci a karawa = Amurka izinin karbo bashi daga dala zambar 14 da milyan dubu dari uku, tareda amincewa kan shirin zabtare magudan kudade da Amurka take kashewa. Amurka zata gaza biyan bashi dake kanta idan bata sami izinin kara gurbin karbo rance nan da 2 ga watan Agusta.