Masu zanga-zanga da yawan su sun rike ko kuma sanya sutura mai launin Ja da Fari, alamar jam’yiyar adawa, suna cewa “Yanci” da “ba zamu manta ba” yayin da suke tattaki a birnin na Minsk. Sun taru na dan lokaci kadan a kusa da fadar shugaban kasar kafin su watse ba tare da tashin hankali ba.
Yayin da kafar yada labarai ta kasar ta sanar da adadin masu zanga zanga dubu 200,000 ne, kafafen watsa labarai da suke bayan kungiyoyin hamayya, sun yi kiyasin cewa wadanda suka shiga zanga-zangar sun kai dubu 100,000 a cewar kamfanin dillacin labaran kasar Faransa.
Tun ran 9 ga watan Agusta a ka fara zanga zanga, yayin da Lukashenko ya yi ikirarin lashe kashi 80 cikin dari, na kuri’un da aka kada. Jam’iyyun adawa sun yi zargin cewa an tafka magudi.