Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Yunkurin Kulla Dangantaka Takanin Isra'ila Da Daular Larabawa


Shugaban Kasar Aurka Donald Trump
Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

Gwamnatin shugaba Trump za ta aike da manyan jami’ai 2 a Gabas ta Tsakiya a wannan makon, tare da zimmar karfafa yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa, domin kafa dangantakar jakadanci.

Jami’an diflomasiyya 3 sun ce Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da babban mashawarci kuma sirikin shugaba Donald Trump Jared Kushner, sun yi shirin kai ziyarce-ziyarce a lokuta daba-daban kuma a kasahe da dama a yankin a ‘yan kwanaki masu zuwa, domin karfafa sake danganta tsakanin Daular da kuma Isra’ila.

Sakataren Harakokin Wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren Harakokin Wajen Amurka Mike Pompeo

Ana sa ran Pompeo ya tashi a yau Lahadi zuwa Isra’ila, Bahrain, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da Sudan, a cewar jami’an na difilomasiyya da suka nemi a sakaya sunansu saboda ba’a kai karshe ko bada sanarwar jadawalin tafiyar ba. Shi kuwa Kushner, zai tashi ne a karshen makon nan zuwa Isra’ila, Bahrain, Oman, Saudi Arebiya da Morocco.

Ana sa ran ziyarar ta su za ta kai ga ba da sanarwar cimma matsay a cewar jami’an difilomasiyyar, duk da ya ke dukan su suna da manufa akalla daya, ta daidaita al’amuran yarjejeniya da Isra’ila nan gaba kadan.

Babban Mashawarci kuma Sirikin Shugaba Trump, Jared Kushner
Babban Mashawarci kuma Sirikin Shugaba Trump, Jared Kushner

Haka kuma Pompeo ya shirya tattaunawa da ‘yan kungiyar Taliban a Qatar, akan batutuwan da suka tattaunawar zaman lafiya, wanda shi zai kasance muhimmin tafarkin janye sauran dakarun Amurka a Afghanistan.

Fadar sgugaban kasa ta White House da kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba su sharhi akan ziyarce-ziyarcen ba da za su kasance wani mataki na gwamnatin Amurkar na karfafa dinke baraka tsakanin Daular Larabawa da Isra’ila, duk kuwa da cewa ba’a sami cimma daidaita ba akan tankiya tsakanin Isra’ila da Palasdinu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG