Mutane da dama sun taru a Tehran babban birnin kasar Iran yau Litinin don nuna juyayin mutuwar Janar Qassem Soleimani, yayin da wanda ya maye gurbinsa ya sha alwashin daukar fansa akan harin da Amurka ta kai wanda ya hallaka shi, a kuma daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke barazanar kai hari kan wuraren tarihin Iran idan har kasar ta mayar da martini.
“An kyalesu su kashe mutanenmu da azabtar da su da kuma dasa boma bomai a gefen hanya dake hallaka mutanenmu, kana mu ba mu da iko mu kai hari kan cibiyar al’adunsu, hakan ba za ta yi wu ba", in ji shugaba Trump a yayin wata ganawa da ya yi da manema labaru a cikin jirgin saman Air Force One a daren jiya Lahadi.
Shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta fada a cikin wata wasika da ta turawa abokan aikinta na jam’iyyar Democrat cewa, majalisar za ta cimma wata matsaya game da yadda za su rage karfin ikon da Shugaban yake da shi akan daukar wani matakin soji akan Iran.
Pelosi ta kwatanta harin na makon da ya gabata a matsayin “takalar fada” kana ta kuma ce zai jefa dakarun Amurka cikin hadari ya kuma kara ruruta wutar takaddama da ke tsakanin Amurka da Iran.