WASHINGTON, DC - Bidiyon da aka dauka daga sararin samaniya a birnin Landan ya nuna yadda masu alhini suka yi dafifi a bakin rafin Thames da kuma tsallaken gadar Tower Bridge, da ke da tazarar kilomita kimanin 5.6. Jami’ai na sa ran mutune 750,000 za su je yi wa gawar sarauniyar ganin karshe kafin a yi jana’izarta ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022.
Zauren taron na Westminster zai kasance a bude tsawon sa’o’i 23 a kullum don masu kai ziyara, kuma sojojin masarautar ne za su yi gidan wurin.
Ranar Alhamis fadar Buckingham ta fidda tsarin abubuwan da za a yi a hukumace, har zuwa ranar Litinin da za a yi jana’izar. A ranar Juma’a, Sarki Charles III da ’yan uwansa za su yi taron addu’o’i na dare a wurin akwatin gawar mahaifiyarsu da ke Westminster Hall tsawon minti 15, kamar yadda suka yi a farkon mako a lokacin da aka ajiye akwatin gawar a majami’ar St. Giles Cathedral da ke Edinburgh.
Ana sa ran kimanin baki 2,000, ciki har da shugabannin kasashe da sauran manyan baki za su halarci taron jana’izar a Westminster Abbey. Jim kadan bayan haka, kowa a fadin Biritaniya zai yi shiru tsawon minti biyu, don ba ‘yan kasar damar yi wa sarauniyar karramawar karshe.