Dubban Falasdinawa da ke samun mafaka a Shifa - asibiti mafi girma a yankin Zirin Gaza na ta tserewa a ranar Juma’a bayan wani hari da dakarun Isra’ila suka kai da ya fada a farfajiyar asibitin.
Dubun dubatar mutane ne dai ke fakewa a asibitin a cewar Ashraf al Qidra, Kakakin ma’aikatar lafiya a yankin na Gaza.
Hotunan bidiyon da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta da sauran kafafen yada labarai suka tantance, sun nuna yadda mazauna asibitin suke cikin yanayi dimuwa suna guje-guje a wajen asibitin na Shifa, inda anan mutanen da suka fice daga muhallansu suke kwana.
Ita dai Isra’ila ta ce Hamas na da maboya a ciki da karkashin asibitin, har ma kuma sun kafa wata cibiyar ba da umarni a karkashin asibitin.
Hamas da hukumomin asibitin sun musanta wannan ikirari na Isra’ila.
A gefe guda kuma, hukumomin da ke ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Duniya a yankin na Gaza sun ce jama’a sun shiga matsanancin yanayi yayin da adadin fararen hula da ke mutuwa ke karuwa.
Hukumomin sun kuma ce ma’aikatan agaji na Majalisar Dinkin Duniya da ke mutuwa sun kai wani shalli da ba a taba gani ba, yayin da unguwannin yankin ke ta fama da harin bama-bamai, lamarin da yake hana ba jama’a damar su je su karbi agajin ruwa, abinci, da magunguna don su tsira da rayukansu.
Kakakin ofishin da ke kula da tsare-tsaren ayyukan jin kai, Jens Laerke, ya fada a ranar Juma’a cewa, daukacin yankin na Gaza na cikin duhu tun daga ranar 11 ga watan Oktoba bayan da aka katse ayyukan samar da wutar lantarki aka kuma hana shiga da man fetur yankin.
Isra’ila ta kaddamara da hare-harenta a yankin na Gaza ne tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba da ya halaka mutum sama da 1,400, mafi akasarinsu fararen hula.
Kazalika Hamas ta kama mutum kusan 240, wadanda suke garkuwa da su.
Amurka, Birtaniya da kungiyar tarayyar Turai da ke yammacin duniya, duk sun ayyana Hamas a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.