DSS Ta Nemi Jama'a Su Kwantar Da Hankali Bisa Gargadin Da Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yi

Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya da rundunar 'yan sandan birnin Abuja sun nemi jama'a su kwantar da hankali bisa gargadin da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya yayi cewa akwai yiwuwar kai harin ta'addanci a babban birnin tarayya.

Hedkwatar hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato DSS ta nemi mazauna babban birnin tarayyar kasar, Abuja su kwantar da hankali sannan su rika taka tsantsan yayin da suke hada-hadarsu ta yau da kullum.

Wata sanarwa da hedkwatar hukumar ta DSS ta fitar mai dauke da sanya hanun kakakinta Dr. Peter Afunyaya tace ai ko a baya ita ma tasha jan hankalin jama'a akan haka, don haka wannan ba wani sabon abu bane.

Don haka ta ja hankalin mazauna babban birnin da suke kaffa - kaffa inda kuma take tabbatar da cewa tana nan tana aiki ba dare ba rana tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro don tabbatar da kare dukiya da rayukan jama'a.

Ita ma rundunar yansandan babbaN birnin Abuja ta tabbatar da cewa ita ma tana nan tana daukar matakan kare dukiya da rayukan jama'ar birnin.

Kwamishinan 'yan sandan Abuja, CP Babaji Sunday ya shaidawa Muryar Amurkma cewa rundunar tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro na nan na sa idi da zummar duk wani kalubalen tsaro.

A jiya ne ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fidda sanarwa inda ke gargadin yiwuwar samun harin ta'addanci a Abujan, sanarwar na cewa akwai yiwuwar kai hari akan ofisoshin gwamnati, makarantu cibiyoyin tsaro, kasuwanni da otal- otal.

Sauran wuraren sune tasoshin mota, filayen wasanni, gidajen abinci, manya manyan shagunan yin sayayya, gidajen barasa, cibiyoyin shakatawa da sauran wuraren taruwar jama'a.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

DSS Ta Nemi Jama'a Su Kwantar Da Hankali Bisa Gargadin Da Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yi