DSS Ta Fara Binciken Dakataccen Shugaban EFCC, Abdurrasheed Bawa

  • Murtala Sanyinna

Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta gayyaci dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Abdurrasheed Bawa.

Bawa ya isa hedikwatar hukumar ta DSS da ke Abuja ‘yan sa’o’i da suka gabata don amsa gayyatar da aka yi masa.

Mista Peter Afunanya, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya tabbatar da gayyatar da aka yi wa Bawa, ya kuma jaddada cewa, yana daga cikin hanyoyin gudanar da bincike kan dimbin zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa Bawa.

Wannan lamari na zuwa ne kuma 'yan sa'o'i kalilan bayan da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya dauki matakin dakatar da Abdulrasheed Bawa daga mukaminsa na shugaban hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC

A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya tura wa manema labarai, ya bayyana cewa shugaban kasar ya bayar da izinin dakatarwar ne domin a samu cikakken bincike kan yadda Bawa ya gudanar da ayyukan hukumar a lokacin sa.

A bisa umarnin shugaba Tinubu, an umurci Bawa ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar. Wannan tsari zai bada damar ci gaba da aiki a ofishin shugaban hukumar har sai an kammala bincike.

Hukumar EFCC dai tana taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun kudaden kasa da kuma tabbatar da cewa an magance laifukan tattalin arziki yadda ya kamata.

An nada Abdulrasheed Bawa a matsayin Shugaban Hukumar EFCC a watan Fabrairun 2021. Sai dai an dakatar da shi daga mukaminsa a watan Yunin 2023 sakamakon zargin cin hanci da rashawa.