WASHINGTON, D.C —
Kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa a Amurka, Dr. Anthony Fauci ya fada a ranar Talata 23 ga watan Yuni cewa, ba a umurce shi da sauran membobin kwamitin yaki da coronavirus na White House da su sassauta gwajin cutar ba, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya ce ya yi.
Kalaman Fauci sun zo ne 'yan sa’o’i bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya hakikance kan cewa da gaske ya ke game da kalaman da ya yi a wurin yakin neman zabensa a Tulsa da ke Oklahoma a ranar Asabar, lokacin da ya ce ya bukaci gwamnatinsa ta sassauta gwaji saboda karin gwaji zai bayyana karin masu kamuwa da cutar.
Tuni dai Jami'an fadar White House suka yi kokarin janye kalaman nasa, suna masu cewa ba kalaman da ya kamata a dauka da muhimmanci ba ne.