Donald Trump Zai Yi Aiki da Ben Carson A Gwamnatinsa

Ben Carson wanda ya fafata da Donald Trump a zaben fidda gwani na jam'iyyarsu ta Republican

Sabon shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump ya zabi daya daga cikin mutanen da suka yi takara da shi a zaben fitarda gwani na jam’iyyarsu ta Republicans, Ben Carson, ya zamar mishi sakatare (watau ministan) Ma’aikatar Gidaje Da Raya Birane na Amurka, wacce a takaice ake kira HUD.

Carson, 65, wanda Likita ne da yayi ritaya, bai da wata kwarewa a fasalin harakokin gidaje amma shi kansa ya rayu ne a cikin gidajen haya na gwamnati, irin wadanda wannan ma’aikatar da ake son damka mishi ke kula da su.

A can baya, wasu shekaru da suka wuce, ya sha sukar lamirin akidar gidajen gwamnati da yace suna sa mutane na dogaro akan gwamnati maimakon kawunansu, har yake cewa kwanda a a rinka karfafawa mutane hanyoyin da zasu iya tsayawa kan kafafunsu.

A lokacinda shi da Trump suka fara yakin neman zaben fitarda gwani na wanda zai tsayawa jam’iyyar su ta Republican a matasyin dan takaranta na shugaban kasa a zaben da aka kamalla, akwai lokacinda Ben Carson ya tsere wa Trump a farin jinin jama’a, amma daga baya sai tagomashin nashi ya zo ya fara rauni, abinda yassa karshenta ya fice takarar.

Carson dai shine bakar fata na farko da Donald Trump ya gabatarda sunansa a matsayin wanda yake son ya baiwa irin wannan mukamin na Minista.