Da yake jawabi a wajen wata holewar kade-kade da wake-waken jajibirin rantsar da shi da aka shirya jiya Alhamis da marece a gaban hubbaren tunawa da tsohon shugaban Amurka Lincoln dake nan Washington, Trump yace shi bai damu ba ”ko a yi ruwan sama a yau, ko kada a yi”, shi ya tabatta yau Jumu’a, ranar rantsar da shi, rana ce mai haske wacce kuma duk idon duniya baki daya zai koma kan Amurka saboda shagalin da ake shirin somawa na rantsarda shi.
Trump yayi wannan kalamin ne a sanadin hasashen da masana yanayi suka yi na cewa watakila yau za’ayi ruwan sama, kuma za’a kara sanyi.
Sabon sakataren watsa labarai na fadar White House ta shugaban Amurka, Sean Spicer yace har yanzu Donald Trump na ci gaba da yin chanje- chanje ga jawabin da zaiyi a wajen bikin daukar rantsuwar tashi (da misalin karfe goma-sha-biyun ranar) yau Jumu’a akan matakalan Majlaisar Dokoki.
Haka kuma Spicer yace ana kamalla rantsarda shi, Trump zai soma rattaba hannu akan dokokin da zasu chanja abubuwa da yawa da yake son chanjawa a Amurka – ciki harda abubuwa da dama da shugaba mai barin gado Barrack Obama ya aiwatarda a lokacin mulkinsa.