Donald Trump Ya Rufe Gwamnatin Amurka

Shugaba Trump

Gwamnatin tarayyar Amurka rufe ayyukan wane bangarenta, kamar yanda shugaba Donald Trump ya fada a baya cewa zai yi alfahari ya rufe ayyukan gwamnati idan har 'yan majalisa suka ki amincewa da bukatarsa ta dala biliyan biyar domin karfafa tsaron kan iyaka ciki har da batun gina katanga a kan iyakar.

Yazuwa karfe 12 na dare agogon Washington zuwa safiyar yau Asabar kimanin kashi 25 cikin dari na ma'aikatun gwamnati basu da kudin gudanar da ayyuka. Sama da da ayyukan gwamnartin tarayya dubu dari takwas zasu huskanci matsaloli kana sama da rabin wannan adadin ayyukan ne za a yi su ba tare da biya ba.

Majalisun dattawa da ta wakilan Amurka sun dage zamansu a cikin daren jiya Juma’a ba tare da tabbatar da dokar da zai baiwa shugaba Donald Trump dala biliyan biyar da ya hikikance yana bukata ya gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico da ma wasu kudaden da wasu hukumomin gwamnati zasu gudanar da ayyuka.

‘Yan majalisar dai suna da har cikin daren jiya Juma’a su tabbatar da dokar kashe kudaden gwamnati, amma kuma sun dage zamansu har izuwa yau Asabar da rana.

Trump aike da wani sakon Twitter na bidiyo yana mai cewa zamu rufe gwamnati. Ya kuma ce dole mu rufe saboda bamu da wani abin yi a kan haka.