"Ya haikance kan haka" kakakin Fadar ta White House Sean Spicer, ya gayawa manema labarai kwana daya bayan da shugaban na Amurka ya sabunta batun lokacin da ya shriya wata liyafa ga wakilan Majalisar Dokokin Amurka, inda ya nanata ikirarin da tuni aka karyata cewa, bakin haure miliyan uku zuwa biyar ne suka kada a kuri'a ga abokiyar takararsa Hillary Clinton. Spice bai nuna wata shaida da zata gaskanta haka ba. Da 'yan jarida suka matsa domin jin shaidar da Trump yake da ita, Spicer yace "Trump ya juma da imani kan haka, saboda bincike da aka gudanar da wasu bayanai da yake da su."
Amma jami'an zabe da suka yi nazarin sakamakon zaben da aka yi ranar 8 ga watan 11, suka ce kusan za'a ce babu rashin gaskiya da aka tafka a zaben, kuma koma da akwai bai kai abunda Trump yake ikirari ba.
Ahalinda ake ciki kuma mutuminda shugaban Amurka Donald Trump ya zaba ya zama ministan kiwon lafiya, dan majalisa Tom Price ya fuskanci zafafan tambayoyi a yayinda ake ci gaba da muhawara kan dokar kiwon lafiya da tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya zartas.
Haka nan Majalisar Dattijan ta amince da Dr. Ben Carson tsohon dan takarar shugabancin Amurka wanda ya kara da Donald Trump a zaman ministan gidaje. Carson dai likita ne wanda yayi ritaya.
Haka nan majalisar ta amince da Nick Haley a zaman jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, tuni ta bayyana goyon bayanta ga kaurar da ofishin jakadancin Amurka daga TelAviv zuwa birnin Qudus, mataki da ake gani yana iya sabunta rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.