Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jami’iyar Republican Donald Trump, wanda ke dada fuskantar matsaloli a kokarin da yake na lashe zaben, yanzu ya juya yana zargin abokiyar karawarsa Hillary Clinton da cewa tana shirya tattara ra’ayoyin jama’a na karya don aga tamkar itace kan gaba.
WASHINGTON, DC —
Yace kuri’ar ra’ayoyin karya ne da kafofin labarai na karya suke kirkikrowa don su kashe mishi kasuwa. Trump dai ya yi wa’yanna kalamai ne alokacin da yake zantawa da dimbin manoma a jihar Florida, jihar da dole ne ya yi nasara a cikinta in yana son cin zaben na ranar takwas ga watan gobe na Nuwamba.
Trump yace ya tabattara shine zai yi nasara a wannan zaben. Sai dai kuma wadanan kalaman nashi suna zuwa ne kwanda daya bayanda shugabar kyamfen dinsa, Kellyyanne Conway da kanta ta fito tace suna bayan Hilary Clinton wacce ke ci gaba da kokarin kafa abin tarin zama mace ta farko da ta taba darewa kan kujerar shugabancin Amurka.