Donald Trump Na Neman Goyon Bayan Majalisa

Shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyara Majalisar Dokokin Amurka a yau Talata inda zai gana da sanatocin jam’iyarsa ta Republican domin neman goyon bayansu

Yayin da ake shirin kada kuri’a kan kudirin neman sauyi a fannin harajin Amurka, wanda za a yi cikin makon nan, shugabannin majalisar dattijai sun gana da shugaba Trump, inda suka bayyana aniyarsu ta kada kuri’ar samar da sauyi a fannin haraji, wanda zai rage kudaden harajin da ake cajin kamfanoni a mataki na dindindin, da kuma rage harajin da mutane ke biya na dan wani lokaci.

Ana kuma sa ran wannan kuduri zai kara sama da Dala Triliyan Daya akan basussukan Amurka.

“Niyyarmu ita ce mu kada kuri’a akan wannan kuduri na haraji.” Inji shugaban masu tsawatarwa John Cornyn da ya fito daga jihar Texas.

“Muna sa ran za mu samu kuri’u 50,” a cewar shugaban kwamitin kudade, Orrin Hatch na jihar Utah.

Wani dan Republican daya, wato Ron Johnson na jihar Winsconsin, ya nuna adawarsa da kudurin.

Sabbin rahotanni sun ruwaito wasu na hannun daman Steve Daines na jihar Montana yana cewa dokar za ta dadadawa manyan kamfanoni ne kawai.

Baya ga haka wasu sanatoci ‘yan jam’iyar Republican da dama sun nuna matukar damuwarsu kan yadda za a kara kudaden akan basussukan Amurka, amma kuma ba su bayyana yadda za su kada kuri’unsu ba.