Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta ce shugaba Donald Trump da sarkin Saudiyya Salman bin Abdul’ziz, sun tattauna ta wayar talho, kuma suka jaddada bukatar da ke akwai ta hadin kan kasashen yankin Gulf biyo bayan shawarar da kasashen larabawa suka yanke na katse hulda da kasar Qatar
WASHINGTON D.C. —
A wata sanarwa da aka fitar da yammacin jiya Talata, tace shugabannin biyu sun tattauna kan muhimmancin dakile hanyoyin samun kudaden kungiyoyiin ta’addanci, da kuma kare musu hanyoyin yada akidojinsu a yankin.
A wasu kalamai da shugaba Trump ya kafe kafar Twitter, yayi kokarin nuna cewa shine makasudin ya sa kasashen larabawa karkashin jagorancin Saudiyya, suka yanke hulda da kasar Qatar wadda a nan ne kasar Amurka ke da babban sansanin soja a gabas ta tsakiya.
Da yake nuni da jawabin da yayi a Riyadh watan da ya gabata, inda yayi kira shugabannin musulmai da su tashi tsaye wajen yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda.