Makon da ya gabata aka sami rahotannin garkuwa da kuma kashe kananan yara biyu da ya hada da Hanifa Abdullahi ‘yar shekaru biyar da ake zargin mai makarantar da ta ke zuwa a birnin Kano, ya yi garkuwa da ita ya kuma kasheta. Da kuma Asama’u Shu’aibu wata karamar yarinya ‘yar shekaru 8 da ake zargin masu garkuwa sun kashe a Zaria, bayan karbar sama da Naira miliyan uku kudin fansa daga mahaifinta.
Wannan ba shine karon farko da aka yi garkuwa, aka kuma kashe karamin yaro a Najeriya ba, sai dai ya kasance karon farko da lamarin ya dauki hankalin al’umma, da ya yiwu, ya kai ga daukar matakin da zai kawo sauyi mai dorewa.
Bakin da muka gayyata domin neman sanin masababin wannan lamarin da kuma hanyar maganceta sun hada da, Hajiya Balaraba Abdullahi ‘yar fafatukar kare hakkokin mata da kananan yara, da masanin shari’a Barista Mainasara Kogo Umar, da kuma da Sheikh Muhajadina Sani Kano.
Saurari cikakken shirin:
Your browser doesn’t support HTML5