Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda Sun Kama Wadanda Suka Kashe Hanifa A Kano


'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya (AP)
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya (AP)

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wadanda suka yi garkuwa tare da hallaka Hanifa Abubakar mai shekaru biyar da haihuwa da aka sace a shekarar da ta gabata.

An kama Abdulmalik da Hashim ne wanda suka kashe ta, tare da saka ta a cikin buhu suka kuma binne ta a wata makaranta dake Tudun Murtala, a karamar hukumar Nassarawa.

Yarinyar mai suna Hanifa an yi garkuwa da ita ne a watan da ya gabata wato 4 ga watan 12, shekara ta 2021. Maharan dai sun kira iyayen Hanifa Abubakar ne aka sanar da su cewa an yi garkuwa da 'yarsu, kuma suna neman kudi naira miliyan shida kafin a sake ta.

Daga bisani an kama mutane biyu, Abdulmalik Muhammad Tanko, mai shekaru 34, da kuma Hashim Isiyaku, mai shekaru 30 da ke Unguwar Tudun Murtala, wadanda Jami'an 'yan sandan Farin Kaya suka kama su.

Makarantar 'Yan Gana, Tudun Murtala
Makarantar 'Yan Gana, Tudun Murtala

Abdulmalik ya tabbatar da cewa Hanifa dalibarsa ce, kuma tana karatu a makarantar da yake koyarwa. Ya ca ya boye ta ne a gidansa na tsawon sati biyu, yayin da daga baya da aka dinga zargin sa da kama ta, shi ne ya sa ya ba ta guba ta sha.

"Da na gane abokan aikina sun fara zargi na, shi ne na yanke shawarar ba ta maganin bera" a cewar Abdulmalik

A yayin da Hashim kuma ya ce shi an ba shi umarni ne ya haka kabari da za a bunne wani bari da aka yi.

"Abdulmalik ya kira ni da cewa matar makwabcinsa ta yi bari, don haka in zo in haka musu kabari da za a bunne barin"

Tun fari dai Abdulmalik ya nemi Hashim da su yi garkuwar amma Hashim ya ki amincewa.

"Abdulmalik sun hada baki ne da abokin laifinshi mai suna Hashim, suka dauke ta suka je suka bunne ta, a yanzu Alla ya ba mu nasarar gano ta a yau ranar 20 ga watan Janairu, shekara ta 2022" In ji Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano Haruna Abdullahi Kiyawa.

Ya kara da cewa tuni aka mika su ga hukuma don fuskantar hukunci.

XS
SM
MD
LG