Abdulmalik wanda ake zargi da garkuwa da kuma kashe Hanifa, ya bayyana cewa, an sa Hanifa a cikin buhu ne wanda ba shi da girma sosai da ya zama dole kafarta ta tankware. Ya ce da yake ita karamar yarinya ce kuma buhun yana da fadi sai aka dan tankwara kafarta yadda dukan jikinta zai shiga buhun amma babu wanda ya dauki wuka ya illata jikinta.
Bisa ga cewarshi, tankware kafafunta kafin sa ta buhun da aka binne ta a ciki, ya sa lokacin da aka tono ta, aka ga kamar an karya gababuwanta, amma a Zahiri ba wanda ya daddatsa ta ko wani abu makamancin haka.
Ya kuma bayyana cewa, an cire rigar sanyi da baje, da kuma hijabin Hanifa ne daga jikinta bayan ta mutu, aka rika aikawa iyayenta a matsayin shaida domin neman kudin fansa. Dangane da lokacin, da kuma wurin da Hanifa ta rasu, Abdulmalik ya ce, ta kwana biyar a gidanshi tare da iyalinshi kafin ya fitar da ita zuwa wani wuri inda ta kwana daya, kafin ta cika ranar goma ga watan Disamba, watau kwana shida bayan yin garkuwa da ita.
A wata hira da aka yi da shi a baya, Abdulmalik ya bayyana cewa, babu wata alaka da ayyukan asiri a garkuwa da kuma kashe Hanifa. Bisa ga cewarshi, ya samu kanshi a cikin mawuyacin halin rayuwa ne, inda ake bin shi bashi da ya hada da kudin hayar ginin makarantar da kuma albashin ma’aikata, ya kuma rasa mafita, dalili ke nan da ya yanke shawarar yin garkuwa da Hanifa da tunanin samun kudin da zai fita daga matsalolin kudin da ya ke ciki.
Ya kuma bayyana cewa, ya yi amfani da Naira dubu saba’in da ‘yan kai daga cikin dubu dari da iyayen Hanifa suka fara bashi a matsayin kudin fansa kafin kama shi, wajen biyan kudin albashin ma’aikatan makarantar shi. Sai dai bai bayyana abinda ya yi da sauran canjin ba.
Shi dai abokin shi, wanda a da, yake aikin gadi a makarantar, Hashimu Ishiyaku, ya bayyana cewa, Abdulmalik ya biya shi Naira dubu daya domin haka rami da kuma binne Hanifa da ya yi.
Da aka tambaye shi yadda ya ke ji da aka kai shi kotu, Abdulmalik ya bayyana cewa, tun kafin kawo shi kotu ya shiga halin kakanikayi. Yace ya shiga hali na tashin hankali, domin duk wanda ya san shi a baya, ya san shi ba mutum ne mai son tashin hankali ba. Abdulmalik ya bayyana cewa, lamarin ba abu ne na jin dadi ba. Ya kuma tabbata su ma (iyayen), ba zasu ji dadi ba.
Dangane da kama shi da kai shi kotu, Abdulmalik ya ce, “tun ma kafin a kawo ni kotu, na riga na yanke shawarar cewa, zan fito bisa radin kaina in fada. Kuma tunda na fito na yi haka abinda na ke jira in gani shine kawai kotu ta tabbatar da adalci irin na ta.”
Abdulmalik Mohammed Tanko, ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar ‘yar shekar biyar ne ranar 4 ga watan Disamba ta wajen daukar ta a keke Napep, tana kan hanyar komawa gida bayan tashi.