DOMIN IYALI: Abinda Al'ummar Jamhuriyar Nijar Ke Son Gwamnati Ta Sa Gaba Wannan Shekarar-Janairu, 05, 2023

Alheri Grace Abdu

A yunkurin shirin Domin Iyali na haska fitila da kuma nazarin matsaloli da ke ci wa al’umma tuwa a kwarya, da nufin jawo hankalin masu ruwa da tsaki a su dauki matakan kawo sauyi, yau shirin zai fara tashi a Jamhuriyar Nijar inda muka nemi jin inda jama'a ke bukata hukumomin kasar su sa gaba, da kuma kara maida hankali a kai.

Batutuwan da suka ambata sun hada da matsalolin tsaro, harkokin ilimi, shan miyagun kwayoyi, samar wa matasa aikin yi da dai sauransu.

Saurari cikakken shirin domin jin abinda wadanda wakiliyarmu Tamar Abari ta zanta da su suke cewa:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Abinda Al'ummar Jamhuriyar Nijar Ke Son Gwamnati Ta Sa Gaba