Dole Ne A Dauki Matakan Gaggawa Masu Dorewa Kan Dumamar Yanayi A Duniya - Masu Ruwa Da Tsaki 

Ana gudanar da ranar muhalli ta duniya ne a duk ranar 5 ga watan Yunin kowacce shekara kamar yadda majalisar dinkin duniya ta ware don karfafa aikin wayar da kan jama'a da kuma daukar matakan da suka dace don kare muhalli.

ABUJA, NIGERIA - A ci gaba da murnar zagayowar ranar muhalli ta duniya da aka gudanar a ranar Lahadi, jami'an majalisar dinkin duniya, daliban makaranta, masu ruwa da tsaki a Najeriya, da kungiyoyin fafutukar kawo mafita ga matsalolin dumamar yanayi sun gudanar da taro don yin kira ga mutane a ciki da wajen Najeriya da su dauki matakan da suka dace cikin gaggawa don samar da mafita ga matsalolin dumamar yanayi.

Babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mattias Schmale, ya bayyana cewa lokaci na kurewa a aikin kare muhalli a fadin duniya sakamakon yadda matsalolin dumamar yanayi ke karuwa kuma ya zama wajibi kasashen duniya su dauki matakan gaggawa don samo mafita mai dorewa, la’akari da cewa babu inda dan'adam ke da shi face doron kasa.

A wani bangare kuma, wani matashi mai aikin dasa bushiyoyi a karkashin kungiyarsa ta Panacea, Dahiru Muhammad, ya yi bayani a kan batun dumamar yanayi.

An dai fara gudanar da bikin ranar muhalli ta duniya ne a shekarar 1973, bikin da ya kasance wani dandalin wayar da kan jama'a kan al'amuran muhalli da suka hada da gurbatar ruwa, yawan jama'a, dumamar yanayi, kashe-kashen namun daji da dai sauransu.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Dole Ne A Dauki Matakan Gaggawa Masu Dorewa Kan Dumamar Yanayi A Duniya - Masu Ruwa Da Tsaki