Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.
Yau za a ji amsar tambaya mai cewa, “Don Allah voa hausa, ku tambayamin masana, ko wace kasa tafi sanyi a duniya.”
Mai tambaya: GARBA NAHALI KAMBA, Unguwar Dogon Rini, Kamba jahar Kebbin Najeriya.
Za kuma a ji maimaicin tambayar nan game da comrade mai cewa: "Assalama alaikum Sashin Hausa na Muryar Amurka. Don Allah ku yi min karin haske kan Kalmar ‘Comrade.’
Shin wane ne comrade?
Me kalmar comrade (kwamrad) ke nufi?
Shin wadanne alamomi comrade (kwamrad) ke da su?
Ta yaya aka samu wannan sunan; kuma a wace shekara?
Wai da gaske ne comrade (kwamrad) bai da aikin yi?"
Masu tambayar kaka Mai Yidi da Alhaji Bukar Gursuma Damasak, jijar Bornon Najeriya.
To bari mu fara da mai tambaya kan kasar da ta fi sanyi a duniya. Idan mai tambayar, Malam Nahali Kamba, na tare da mu, ga amsarka da wakilinmu a Adamawa, Mohammad Salisu Garba, ya samo daga Dr. Madube Tumba Kwabe, da ke koyar da darasin kimiyyar Yanayi da Muhalli ko jografiyya a Kwalejin Horas da Malamai ta Gwamnatin Tarayya (FCE, a takaice), da ke Yola, Adamawa, Najeriya.
Sai kuma maimaicin amsar tambayar su Kaka Mai Yidi; da Alhaji Bukar Gursuma Damasak, game da kwamrad (Comrade). Idan ana tare da mu, za a ji maimaicin amsoshin da wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Garba, ya samo daga wurin Dr. Babikwai Girei, wanda ya ce.
A sha bayanai lafiya: