“Ba za a iya warware korafe-korafen ta hanyar karin rikice-rikice ba. Wannan haka ya ke a fili. Kuma yayin da rashin zaman lafiya ke karuwa a wurare irin su Sudan da Nijar, dole ne bangarorin da ke cikin Libya su guje wa ayyukan da za su kara haifar da tashin hankali."\
Abin da ya fi kyau ga al'ummar Libya ita ce karfafa goyon bayan zabe da sauri, in ji Ambasada Thomas-Greenfield:
"Dukkan jam'iyyu - Majalisar Wakilai, Majalisar Dokokin, Gwamnatin Hadin kan Kasa, Sojojin Libiya, da Majalisar Shugaban kasa - na bukatar su taru don yin sulhun da ake bukata don gudanar da zabuka."
Al'ummar kasar Libya a shirye suke su yi sulhu da za su samar da zabe da kwanciyar hankali, a cewar Ambasada Thomas-Greenfield, "Don haka, a shirye muke mu ba da goyon baya ga kafa gwamnatin rikon kwarya ta fasaha wacce aikinta kawai shi ne ta kawo kasar ga zabe mai inganci."
Game da "gudanar da kuɗaɗen shiga, muna samun ƙarfafa ta hanyar haɗin gwiwar Babban Bankin da kuma kafa Babban Kwamitin Kuɗi," in ji Ambasada Thomas-Greenfield. "Wannan kokarin da Libya ke jagoranta zai tabbatar da cewa babu wani mutum guda da ke da iko na musamman kan kashe kudaden jama'a. Kuma hakan zai taimaka wajen magance korafe-korafe kan yadda ake raba kudaden shiga.”
Amurka na samun kwarin gwiwa ta kokarin kawar da sojojin kasashen waje, mayaka, da sojojin haya - da kuma ci gaba da kokarin ganin an kawar da makamai, da kuma tsarin sake hadewa cikin jama'a. Ambasada Thomas-Greenfield ta kara da cewa "ci gaban da aka samu a baya-bayan nan game da kafa wata runduna ta hadin gwiwa da za ta iya sintiri a kudancin kasar za ta taimaka wajen tabbatar da tsaron iyakokin kasar Libya da kuma hana barkewar rikicin yankin."
Ambasada Thomas-Greenfield ta bayyana cewa, Amurka za ta ci gaba da haskawa kan mummunan tasirin da kungiyar Wagner ke yi a Libya da Afirka baki daya:
"Bari mu fito fili: kasashen da ke da aikin Wagner a cikin iyakokinsu sun sami kansu cikin talauci, rauni, da rashin tsaro. Muna ganin haka a Mali, Burkina Faso, Nijar, da Sudan. Shugabancin Wagner bai boye burinsa na samun wani matsayi a Afirka ba, da kuma rashin mutunta yankin Libya."
Ambasada Thomas-Greenfield ta ce "Al'ummar Libya sun cancanci samun sauyi, sun cancanci ci gaba, sun cancanci fata. Kuma ya rage ga shugabannin Libya su dauki mataki tare da samar da sakamako."