Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas Greenfield ta ce "A yau, duk da kayan aikin zamani da muke da su, muna fuskantar matsalar karancin abinci a duniya da na taba gani." "A Afirka, daya daga cikin mutane biyar ba ya samun isasshen abinci mai gina jiki - daya cikin biyar."
Rashin wadatar abinci yana nufin iyalai ba sa iya tanada abinci ga 'ya'yansu. Yana nufin yara ba sa samun abinci mai gina jiki da suke bukata don samun nasara a makaranta. Kuma a cikin mafi munin yanayi, yana nufin yunwa. Kuma yunwa tana nufin mutuwa.
"Don haka dole ne mu kudura aniyar kawar da yunwa."
Domin cimma wannan burin, in ji ta, dole ne mu kalli abin da ke haifar da karancin abinci tun da farko.
Ina ganin dalilai guda hudu: abin da na kira "E" da "C" uku. Makamashi. Yanayi. CUTAR COVID. Kuma Rikici.”
"Farashin makamashi ya tashi a cikin shekarar da ta gabata." Kuma saboda makamashi yana da muhimmanci wajen samar da abinci, hauhawar farashin makamashi yana nufin abinci mai tsada.
Na farko "C" yana nufin sauyin yanayi.
“Matsalar sauyin yanayi, matsala ce da ta shafi bala’o’i, na ambaliya da guguwa da kuma zafin rana. Amma kuma kai tsaye yana haifar da matsalar karancin abinci.”
Na biyu "C" shine COVID.
Jakadiya Thomas-Greenfield ta ce annobar "COVID-19 ta kara nawaita tsarin." "Kafin COVID, mutane miliyan 100 ba su da abinci. Shekaru uku bayan haka, a cikin shekaru uku kawai, adadin ya haura zuwa sama da mutane miliyan 190.”
"Sai kuma "C" na uku, wanda na yi imani shi ne sanadin yunwa," in ji Jakadiya Thomas Greenfield. “Yunwa ce ta haifar da rikici. Yunwa da ake haifarwa da gangan. Yunwa da aka yi amfani da ita a matsayin makamin yaki.”
Jakadiya Thomas Greenfield ta ce "Duk wadannan matsalolin - makamashi, yanayi, COVID, da rikici - sun hade suka haifar da mummunan rikicin yunwa irin da ba mu taba gani ba a rayuwarmu."
A karshe, saboda rikice-rikice na iya sanya makamin yunwa da tilasta wa mutane barin gidajensu, wanda ke kawo matsala ga tsarin abinci na kasashen da ke kewaye, Jakadiya Thomas Greenfield ta ba da sanarwar sama da dalar Amurka miliyan 127 a cikin karin tallafin jinkai “domin tallafawa ‘yan gudun hijira, masu neman mafaka, da ‘yan gudun hijira, da ba su da alaka da wata kasa, da kuma mutanen da s uke fuskantar tsangwama a fadin Afirka."
"Yanzu ne lokacin da za a yi aiki tare tsakanin gwamnatoci, da d kasashe, da kuma tsakanin mutane, don kawo karshen yunwa," in ji ta. "Yanzu ne lokacin da za a kulla kawance tare da kungiyoyin farar hula, kamfanoni masu zaman kansu, don ciyar da mazauna waje, don cin gajiyar sabbin fasahohi da ingantattun dabaru, don tsara hanyar samar da abinci mai dorewa nan gaba."