A yayin da wasu al’ummar jihar Kaduna ke ci gaba da ciwon baki game wannan doka, sai dai fa tambayar da wasu keyi shine anya kuwa al’umar jihar suna da masaniya game da dokar? Hakan yasa wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikira, zantawa da wasu ‘yan jihar.
A cewar Mansur Sani, wani dan jihar Kaduna yace shi dai yana jin labarin wannan dokane cikin labarai. Shi kuma Usaini Musa Aliyu cewa yayi ya saurari cikakken bayani game da ma’anar dokar da yadda zata kasance. Sai dai Umar Hassan cewa yayi shi kan bai ma san inda aka dosa ba, kamar sauran mutane dake cewa ba a yi musu cikakken bayanin yadda dokokin zasu kasance ba.
Shin kome ke kunshe cikin wannan doka ta gudanar da wa’azi a Kaduna? Kuma ina batun da ke cewa wasu daga cikin sassan wannan doka sunci karo da sunci karo da wasu daga cikin kudin tsarin mulkin Najeriya. hakan yasa lauya mai zaman kansa Barista Al-Zubair Abubakar, yayi karin haske kan wadannan batu. Inda yace gwamnatin jihar Kaduna na son ta sa dokar kada wanda ya zagi wani don suna da bambamcin ra’ayi ko kungiya ko kuma addini.
Ita dai wannan doka yanzu haka tana gaban ‘yan Majalisu, su kuma al’umar jihar na ta tofa albarkacin bakinsu da kuma jiran lokacin da zata fito.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5